Sunday, March 3, 2019
Me ne Gaskiyar Mutuwar Sambo Dasuki?
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta karyata labarin da ake ta yadawa cewa tsohon mai bai shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro Kanal Sambo Dasuki ya rasu.
Kakakin hukumar Peter Afunanya ya shaida wa kafar talabijin ta kasa NTA cewa labarin karya ne ake yada wa, yana mai cewa "ba wai yana raye ba ne kawai, yana kuma cikin koshin lafiya."
Ya kuma yi Allah wadai da labarin wanda ake ta yadawa a intanet, tare da yin kira ga jama'a su yi watsi da shi.
Sambo Dasuki ya shafe fiye da shekaru uku a tsare. Tun watan Disamban 2015 hukumar DSS ke tsare da shi kan zargin wawushe kudin da aka ware domin sayo makaman yaki da Boko Haram.
Ana ci gaba da tsare Dasuki ne duk da kotun Tarayya ta sha ba da shi beli, har da kotun ECOWAS.,,,,,
Gwamnatin Buhari dai ta dade tana cewa tana ci gaba da rike shi ne saboda ta daukaka kara.
'Yan jaridar da suka ziyarci inda ake tsare da shi sun ce sun yi tozali da shi, inda suka jima suna hira har ya amince aka dauki hotonsa domin karyata labarin ya mutu.
Labels:
Labarai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment