Friday, March 1, 2019

Abinda Ke Yawaita Mace Macen Aure A Al'adan Hausawa



Al’ada wata aba ce wadda ke nuna yadda wasu mutane suke gabatar da rayuwarsu, wadanda suka shafi zamantakewarsu, da aure da suna da biki, da dai sauran wasu al’amuransu. Wata al’adar fifita ta yana da kyau, kamar yadda al’adar kunya da girmama na gaba du wadannan abubuwa ne masu kyau.

Sannan kuma akwai al’adar kayayyakin gargajiya wato sutura wadanda aka gada tun daga Kaka da Kakanni, da dai sauransu. Sai dai ita al’ada ta bambanta daga wannan kasa zuwa waccan, bugu da kari kuma daga wannan harshe zuwa waccan, haka al’amuran suke. Wata al’adar kuwa idan an yi amfani da ita ba za a iya kwashe wa da mara ba, ana dai yi ne kawai saboda cim ma wasu bukatu.
An san ko kadan ba ta da kyau amma ana yi ne kawai. Kafin dai mu kalli wata dadaddar al’ada ya dace mu dan duba baya tukuna ‘ Sai an kada gizo tukunna ake cewa koki ta taso’’ wato maganar aure yadda ake tatike gidan da za su auro. A yi maganar wani abu wai shi na-gani-ina so, ga kuma lefe, kudin sa rana ga kuma maganar wani abu na kudin mazan baya idan ta kasance bazawara ce.
Kai wani wurin ma sai an yi maganar wasu kudade na gaisuwar dangin mahaifiyar budurwar da ake nema da aure da kuma na mahaifinta su ma akwai wani kaso nasu, wanda idan ba a kawo shi ba, ana iya haduwa da matsala. Duk wadannan ba su zama dole ba ne domin su mustahabi ne, maganar kudin sadaki ita ce kowa ya sani ita kuma ce ake magana. Idan aka zo maganar daurin aure ai maganar sadaki ceake farayi, ba maganar wani sabi zarce da wasu kayayyakin al’ada ba.

Idan muka kalli wata dadaddar al’ada wadda har yanzu akwai wuraren da ake yinta wato maganar da ake yi ta tafiya goyon-ciki, wani wurin sai an haihu wani wurin kuma kafin a haihun, ita matar auren mai cikin takan tafi.
Idan amaryar ta samu ciki lokacin haihuwarta ya kusa ta kan tafi gidan mahaifanta ta haihu can, duk wata dawainiyar da ta shafi kula wa da ita da kuma abin da ta haifa a gidan mahaifanta a kan yi duk kuwa da yake gidansu mahaifan mijinta su ma ana tatsarsu kamar hanji sosai da sosai.
Bayan an haihu ne lokacin da ya kamata ace ita maijegon ya dace ta koma gidan mijinta, ba zata koma ba saian yi matawani abu wanda ake kira banti wanda wasu kayayyaki ne wanda a doka ta gargajiya ce wasu ke amfani da ita, ke nuna cewa ita maijegon ba za ta koma gidan mijin ba, sai har gidan shi angon kauri sun sayi wasu kayayyaki, wani wurin ma idan abubuwan da ake bukata ba su cika ba ko da daya ne ya rage sai an kawo shi tukuna, ba a wani yarda ta koma,wadanda ba su iya sa wa, a yi wata maganar komawa gidan mijinta ba sam-sam.
Haka nan iyayenta za su shafa wa idonsu toka kiri da muzu su ki amince wa da ‘yar ta su ta koma gidan mijinta, idan kuma ba sa’a aka yi ba wannan al’amarin ana ji ana gani sai an raba shi ke nan, ana ji ana gani an bar maganar raya sunnar Annabi Muhammadu Salallahu alaihi wasallam. Kodayake dai wani lokacin ma ba laifin mahaifanata ba ne amma ‘yanuwansu ne sukan zama karfen-kafa dangane da komawarta gidan mijinta, duk kuwa yadda suke son junansu sai dai su yi na mai bara wato hakuri. Bugu da kari kuma ga haihuwa abin da ke nuna zuri’a ta fara samuwa ke nan.
Amma duk wannan bata damu wasu ba, su dai su raya al’adar nan wadda bata zama dole ba ne sai an yi ta ba, ana dai biye ma son zuciya wanda kuma bacin zuciya ne a gaba. Ta haka ne ake samun karamar bazawara ko kuma abinda wasu suke kira da sakin wawa saboda ko dai an so ko kuma an ki, haka ana ji ana gani za a kashe auren, ba kuma wanda ya isa ya ce, ba a kyauta ba Daga raba auren nan wata shi ke nan duk yadda aka yi kokari kafin ta samu ta sake yin wani auren, akan dauki lokaci mai tsawo saboda ai su mahaifan nata sun yi mata raunin da yake da wuyar warke wa ne, wanda tamkar cutar kanjamai ce ko kuma kabari salamu alikum.
Duk dai wanda ya zo neman auren ta sai ya tambayi dalilin da yasa ta fito daga gidan mijinta na farko wanda ya wanke ta, ita kuma ta wanke shi. Da kuma ya ji ai ga dalilin da ya yi sanadiyar fito da ita daga gidan mijinta, a hankali zai janye kansa, wanda ita ba laifinta ba ne akidar biyayya ce ga al’ada wadda mahaifanta suka fifita ita ce ta sa ta kasance cikin halin hakan.

Wasu al’adunma sun wuce na gargajiya yanzu an ma dade da shigo wa da na zamani a ciki, wadanda ke nuna yawan akwatuna da aka kawo gidan ita yarinyar da ake, nema da auren.
Koda yake dai ko wanne masaki akwai abokin na shi burmin, hakanan ko wacce randa akwai marfin da zai iya rufe ta, amma wasu ba su lura da hakan. Dalili kuwa ana bude ma wasu hanya ce da wadanda ba su kai kamar su ba, su ce su ma sai an yi masu hakan, da hagu da dama duk suna neman su jagule al’amuran ne gaba daya.
Wanda ya isa a yi magana da wanda bai isa ba, duk abubuwan sun yi kiki-kaka babu wani gaba bare kuma baya, wanda a dalilin hakan ya sa ga mata nan masu yawa zawarawa da kuma ‘yanmata, ana son zuwa amma ana cikin tsoron yin hakan ba kauyen ba, bare kuma birnin.
Abin ya dai kamata a ce zuwa yanzun an fara tunanin yin karatun ta natsu a duba wadanne al’adu ne idan aka ci gaba da tafiya da su za a cim ma buri, wadanna ne kuma idan aka rika tafiyar da su za a rika nutsewa kasa kasa cikin tabon laka, tamkar wanda ya shiga cikin laka da damina.
Duka abubuwan biyu suna da bada matsala amma wani abu daban har yanzu, wadanda suka kalli Arewa maimakon su mike sosai , tafiya suke suna ta kallon Yamma, su kuma wadanda ya dace ko nace sun nufi gabas, sai ga shi suna tafiya suna ta kallo kudu kuma, to duk ina za a je ne da hakan?. Ga al’adun na gargajiya da kuma na zamani duk an tasa su gaba, bayan su ba su ma san hanyar da ya kamata a bi ba.
Ai bai dace ba makaho ya yi wa makaho jagora, amma idan aka samu ko da mai ido daya ne abin a samu dan sassauci don yana gani da hangen yadda ake yin tafiyar. Ana irin wannan kisan mummuken ne ma rayuwar auren wasu a wurare daban daban sai dai ita al’adar nan tafi ta can, kuma kamata ya yi duk da yake dai ya kamata ace tuni an samu lokacin da ya dace ayi watsi da ita al’adar saboda ai ba ko wacce al’ada ba ce ya dace a ce ana yi mata hawan feda ba, sake ne ya fi dacewa.
Ya kamata sarakuna da malamai su yi wani abu wanda zai taka rawa wajen binne duk wasu al’adun da ba su dace ba, saboda idan aka yi tunani za suna haifar da raini maimakon kawo ci gaban al’umma.
Ba kuma wani lokacin da ya fi dacewa a daukin matakin da yafi dacewa kamar yanzu, a koma kan hanyoyin da suka dace, wadanda kuma me Alkur’ani ya ce, ko kuma Hadisin manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce, ba wai maganar wata al’adar da ba ta zama dole a bita ba...,

No comments:

Post a Comment