Wednesday, February 27, 2019
Tsaraba Ga Mata Masu Ciki Domin Samun Sauki Gurin Haihuwar (Ingantaccen Hanya)
Tabbas mata da yawa sukan sha wahala sosai idan watan haihuwarsu ya kama domin Allah kadai ya san cikin irin yanayin da suke shiga. Wannan shafin mai albarka, ya kawo maku wata fa’ida wacce tabbas mun tabbatar da ingancin ta idan aka jaraba in sha Allah za a dace duk mata mace mai shan wahalar nakuda to ta samu Zuma mai kyau kaman cikin Kofi ko cokali 24 ta shanye a take...,
Sannan a samu wani zumar a zuba ruwan zafi a ciki tana shan shi da zafi wannan zai taimaka wajen juya yaro in sha Allah. Hakan yama fi ruwan nakuda karfi, Sai dai kuma in Allah bai yi fitar yaron ba a lokacin amma inba haka ba a take yaron zai fito in sha Allahu. Shi ya sa yana da kyau sosai da zarar cikin mace ya kai wata 7 ta dinga tafasa ‘ya’yan hulba tana zama a ciki kullum sau daya in ya shiga wata 9 ta dinga yi safe da yamma.
Hakan zai taimaka sosai wajen bude kofofin aihuwa kuma da wuya mace ta karu a lokacin aihuwa. Kuma mace za ta samu garin hulba ta kwaba da Zuma tana shan cokali biyu safe da yamma, in sha Allahu za ta samu sauki sosai wajen aihuwa amma kada mace mai ciki ta yi amfani da hulba har sai cikin ya tsufa ma’ana lokacin nakuda saboda hulba tana zubar da yaron ciki.
Allah ya sa mu dace dan Allah duk wanda ya karanta to ya yi kokari ya sanar wa yan’uwa mata saboda a samu saukin nakuda sannan kuma a samu saukin fidar yaro daga cikin mahaifa.
Labels:
Lakanin Mata
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment