ZAN SO BAYAN KUN GAMA KARANTAWA KU YI RUBUTU(COMMENT)
‘Yan’uwa magidanta, su na tambayar me mata su ke so a yi ma su lokacin Jima'i, ko kuma ya za su gane cewa mace ta kai ga tata biyan buqatar, da dai sauran tambayoyi irin hakaDa farko dai ya na da kyau Maigida ya san cewa akwai banbanci girman gaske tsakanin yanayin sha’awar sa da ta Maidakin sa. Maza na kwadayin ibadar aure ne don dadin da hakan zai haifar ma su, Yayin da sha’awar ‘ya mace jin dadin ne ke motso da ita, don haka mace in ba ta jin dadI, ko ta na cikin tashin hankali ko rudI, to ba za ta taba jin motsuwar sha’awa ba balle har ta sami biyan buqata.
Don haka in har maigida ya na son ya taimaki Uwargida wajen farfado ma ta da daskararriyar sha’awar ta, to dole sai ya kasance mai kwantar ma ta da hankali, nuna ma ta soyayya da kuma mutunta.
Sai gabatar da wasanni kafin gabatar da ibadar aure, dole maigida ya daure ya ga dumama maidakin sa sosai, ya kasance nuke cikin sha’awa, ta yadda za ta iya kaiwa ga biyan buqata cikin sauri, domin kamar yadda na fada, sha’awar ‘ya mace a jiqe ta ke kamar jiqaqqen icce, yayin da ta namiji kamar busashshen kara ta ke.
Wannan ne ya sa sha’awar namiji ko da yaushe a kurkusa ta ke, kamar yunwa ta ke da gamsuwar da ake samu bayan cin abinci amma sha’awar ‘ya mace sai bayan an samu gamsuwar cin abincin sannan za a fara jin yunwar.
Kuma kamar yadda kowa ce mace da kalar abincin da ta fi sha’awar ci, kuma kalar abincin na iya canzawa daga lokaci zuwa lokaci, to haka ma sha’awar ‘ya mace; abin da wata ke so lokacin ibadar aure ba shi wata ke so ba, kuma yanayi irin na al’ada ko shigar ciki na canza abin da mace ta fi so lokacin ibadar aure.
Don haka ya na da matuqar alfanu ga Uwargida ta cire kunya ta fada ma maigidan ta abubuwan da ta fi so ya yi ma ta lokacin ibadar aure.Kunya tsakanin ma’aurata na da kyau sosai amma ban da lokacin gabatar da ibadar aure.
Amma in har kunyar ta yi yawa ta yadda Uwargida ba ta iya fada ma maigida irin abubwan da ta ke so, to sai ta bari jikin ta ya yi ma ta magana, shi maigida sai ya yi ta lalube har sai nemo abin da ta fiso ta hanyar amsar da jikin ta ya bayar yayin da ya yi ma ta abin nan.
Da yawa mata na mitar yadda mazan su su ka maishe su kamar wasu abin mallakar su, ta yadda dole kawai su yi amfani da su ko su na so ko ba sa so ba tare da da biya ma su ta su buqatar ba, wannan babban kuskure ne ainun, jin dadin ibadar aure halas ne ga dukkan ma’aurata ba ga namiji kadai ba.
Sannan wasu magidantan na ganin kamar qin gabatar da wasannin ibadar aure wani bangare ne na taqawa, wannan ba haka ba ne, domin an samu Hadisi daga Sayyidatuna Aishatu RA ta na cewa Annabi SAW ya kan sumbace daya daga cikin matan sa, kuma Ya gabatar da salla ba tare da sake alwalla ba. Haka nan su kan yi tsere tare, su yi wanka tare, har aswaki su kan yi da tsinke daya, kuma a bayyane ya ke ba mutumin da ya kai Shi SAW taqawa duk duniya.
Taimakon da Uwargida za ta iya yi ma Kan ta
Da farko Uwar-gida ta fara kai kukan ta ga Allah Azza wa Jallah, ta gaya ma shi matsalar ta, ta kyuatata yabo da godiya gare shi sannan ta nemi waraka daga gare shi.
Uwargida ta cire duk wani rashin so ko jin haushin maigida daga zuciyar ta, indai akwai wannan zai matuqar wahala ta yi sha’awar maigida balle har ta kai ga biyan buqata, wannan ta faruwa ga matan da aka tilasta ma su auren mazan da ba su so, komin irin kyautatawar da mazan ke ma su, tsanar na nan a zuciyar su ba ta gushe ba. In irin haka ta kasance, ya kama ta Uwargida ta san kan ta kawai ta ke cuta da rashin gusar da tsohuwar qiyayyar nan daga zuciyar ta, Allah Ya riga Ya qaddaro shi ne mijin ki, ba abin da za ki yi ki canza haka komin yadda ki ka so, don haka ya na kyau ki kasance mai gode ma Ubangijin ki Allah a cikin ko wane irin hali Ya saki. Dagewa da qin Maigida bayan bakin alqalami ya riga ya bushe rashin godiya ne ga Allah SWT..../
Wata sa’a kuma cigaba a rayuwa da hidimomin rayuwa ne ke daskarar da soyayya tsakanin ma’aurata, rashin soyayya kuwa na daskarar da sha’awar ‘ya mace, don haka ya na kyau Uwargida ta daure ta zama mai rayar da soyayyar ta da mijin ta ako da yaushe, komin wuyar halin shi mijin da kuma canjin da ya na yi kan iya haifarwa. Namiji kamar jariri ne, sai an lallabashi da lallashi da hikimomi da ‘yan dubaru, yadda ki ka san za ki yi haquri da dan jaririn ki komin yadda ya bata ma ki rai ko ya gajiyar da ke, to haka nan za ki yi haquri da maigidan ki, maigidan ki fa hanyar aljannar ki ce, kin sa ko hanyar Aljanna ko qayoyi da kwalabe aka zuba mutum ya bi ta indai za ta kai shi ga shiga aljanna, don haka mata a qara dagewa, a cigaba da son maigida da kyautata ma sa komin wuyar halin sa ko wulaqancin sa, domin wannan hanyar samun frincikin duniya da lahira.
Uwargida ta yawaita cin abubuwa ma su qara sha’awa da ni’ima a jiki irin su madarar shanu, tatacciyar kwakwa, zuma, dabino kunun aya da sauran ‘ya’yan itace da kayan lambu da magunguna da a ke hadawa da hakukuwa daban-daban amma a lura da kyau wajen sayen irin wadannan magungunan domin wasun su su na da illa ga lafiyar jiki musamman wadanda za a ce sai an tura cikin al’aura, yawancin su su na haifar da ciwon daji ko qaba na mahaifa. Haka kuma akwai wadan da a ke sa tsibbu a ciki, don haka duk wani magani da za a ce a tofa ko a rubuta wa su ayoyin alqur’ani, ko wanda za a dafa kaza a ce a yi rami a rufe qashin, da sauran ire-iren su, tsibbu ne, kuma duk wacce ta ti haka to ta saba ma koyarwar Annabin mu SAW.
Sannan ga wani ingantaccen magani mai warkar da duk wata matsala da ta danganci sha’awar ‘ya mace da ‘yammatancin ta. In mace ba ta jin motsuwar sha’awa, zai motso mata da sha’awar ta, ga matan da ko sha’awar su ta motso ta na saurin sauka ba tare da sun cimma biyan buqatar su ba, wannan magani zai sa su runqa kaiwa ga biyan buqatar su akai-akai. Ga matan da zuumar su ta ‘ya mace ta bushe ko jijiyoyin yammatancin su su ka sakki, ga matan da yawan haihuwa ko tsufa ya sa ba sa iya riqe fitsari, wannan magani duk zai warkar ma su da shi, bai da tsada kuma ya na da sauqin samu, sannan garanti ne duk wacce ta yi a yadda a ka ce ta yi, to cikin yardar Allah da amincewar sa za ta ga kyakyawan sakamako. Da fatan za a daure a yi shi kamar yadda a ka ce. Allah kuma ya sa ya kasance sanadiyyar qaruwar farinciki a rayuwar auren ku gaba daya amin.
Shi dai wannan magani ba ci, sha, ko shafa sa a ke ba, wannan magani kamar wani samfurin motsa jiki ne amma na jijiyoyin mahaifa da na al’aura ‘ya mace. Su wadannnan jijiyoyi su na nan shimfide a qasan ‘yammatanci, kuma su ke riqe da qofar ‘yammatanci da kuma hanyar fitar fitsari. Yawan haihuwa na sa wadannan jijiyoyi su sakki, shi ke sa mace ta kasance ba ta iya riqon fitsari, ba ta jin motsuwar sha’awa, kuma ko min qoqarin ta ba ta iya cimma biyan buqata, sannan mijin ta ba ya gamsuwa da ita kamar yadda ya saba a farkon auren su. Motsa wannan jijijyoyi akai-akai na sa su dawo da qarfin su na da, kuma ci-gaba da motsa su na sa zuumar ni’imar yammatanci ta qaru har ta tumbatsa.
Hanya ma fi saui ta koyan yadda za a motsa jijiyoyin shi ne lokacin da a ka je fitsari, sai a buda ko ware qafafuwa sosai sanna a matse fitsarin, kar a bari ya zubo, sai a runqa sako fitsarin da kadan-kadan a hankali ya na fita, kamar cikin qaramin cokali a kowane sakowa, in mace ta yi haka sau ukku zuwa biyar, a hankali za ta fahimci wadannan jijiyoyi kuma za ta ji mazaunin su a jikin ta. Da haka ko ta na zaune ne sai ta runqa qoqarin motsa su, sai ta runqa irin yunqurin da a ke yi in a na son fitar da fitsari.
In Uwargida ta haddace wannan, daga nan sai ta runqa yin haka sau shidda a rana kuma a kowane yi daya ya kasance ta motsa su sau goma ko sama da haka, a hankali in a ka saba sai a qara yawan yin da yawan motsawar.
Da farko kam akwai wahala, sai an dage kuma an cije, amma da an saba a hankali sai ya zama kamar shan ruwan sanyi. Sannan kar don ganin sakamako mai kyau a ce za a dakata, in an dakata a hankali za a koma ‘yar gidan jiya ne.
Kuma maza ma su fama da matsalar saurin fitar maniyyi da wuri za su iya yin wannan motsa jijiyoyin kamar ya zo a sama, InshaAllah zai taimaka ma su qwarai da gaske.
Ga wadanda ke da hali, akwai wani dan abin sarrafa wadannan jijyoyi da aka qera mai suna Kegel Master, wanda in ka yi amfani da shi zai motsa ma ka su ba tare da yunqurin ka ba kamar dai yadda a ka yo injinan motsa jiki. Na san ba kowace kasuwa za a same shi ba, sai a laluba a irin kasuwannin zamani kamar irin su wellcare da ke Kano, InshaAllah za a samu.
Da fatan Allah ya taimaka ya ba da ikon jurewa da dagewa, ya kuma sa a ga alfanun abin amin.
Da Fatan Kuma Zaku Tura Wa Sauran Yan'uwa Domin Suma Su Amfana
Ku Karanta :
No comments:
Post a Comment