Friday, February 22, 2019
Gudumuwar Da Hanta Da Tafarnuwa Ke Bada Ajikin Mutun
Hanta wacce a Turance ake kira da liber tana daya daga cikin nama mafi armashi da tagomashi a idon jama’a. Ta kasance ba ta da karfi domin ba tsoka ba ce kuma ba jijiya ba ce, tana da dandano daban dana sauran nama.
Tsuntsaye, kaji da dabbobi sun kasance suna da hanta kuma duka ana cin hantarsu in bancinda dabbobi da tsuntsayen da aka haramta wa musulmi su ci kamar kolo, kare, alade da sauransu.
Akwai wani bincike da wasu masana kimiyar abinci suka gudanar a kan hantar da ta fi amfani ga jiki, daga karshe sai suka gano hantar kaji sun fi na sauran dabbobin amfani a cewarsu “ Hantar kaza daya tana dauke da sinadarin calories 49, grams 7 na protein, grams 2 na kitse, micrograms 6 na sinadirin B12, micrograms 162 na folate da makamantansu.
Hanta ba ta dauke da yawan maiko kamar na sauran nama.
Tun azal mun jima muna ta jin labarin hanta dama irin yanda mutane suka fi sonta fiye da sauran nama wanda hakan ya sa tafi tsada ko ga masu sana’ar saida nama, wasu na mamakin ace hanta tafi sauran nama kamar zuciya, koda, ciki, hanji da sauransu amfani, ganin cewa ai dukan su nama ne. A nan akwai wasu sinadirrai na daban da Allah ya sanya ga hanta wadanda babu su ga sauran naman. Wannan ya sa masana kiwon lafiya suka bayyana hanta a matsayin wacce tafi kowane nama ko abinci amfani, wannan ilimi ne da hikima ta Allah kuma ta zama magani ga al’umma. Domin hanta tana magani sosai ganin tana kumshe da sinadiran bit A, Iron, Bit B, Bit B12 da sauransu.
Hanta tana kare jiki daga kamuwa da anemia haka kuma idan ana fama da wannan cuta to sai a fake cin hanta in sha Allahu za a dace.
Hanta tana taimaka wa wajen samun haihuwa.
Cin hanta da ganye na maidoda jinin da aka rasa a dalili da jinya na rashin lafiya ko karamcin jini sanadin hatsari ko kuna na wuta.
Cin hanta na sanya mace mai juna biyu ta samu koshin lafiya da isashen sinadirin iron dan amfaninta da jinjirinta.
Cin hanta na kara lafiyar kwakwalwa.
Kasancewa hanta na dauke da sinadirin B12 wanda karamcinsa a jiki lahani ne dan ya kan haddasa kasala da rashin karfin jiki da dushewar aikin kwakwalwa. Dan haka kwakwalwar mu na da bukata da sinadurin B12 dan kauda wadannan matsalolin dana lisafo.
Hanta na kumshe da sinadirin Bit A wanda yake karawa ido lafiya da gani tangaram ba garaye-garaye ba hadi da karawa kassan jiki karfi.
Wanda ke da karamcin jini mace ko namiji, yaro ko babba to sai a rinka dafa masa hanta a hankali yana ci. Domin cin hanta na samar da jini sosai a dalilinta na mallakar sinadirin Iron mai yawan gaske.
Cin hanta na magance matsalolin rikicewar haila ga mata da kuma abubuwan da suka shafi kwakwalwa.
Mata masu juna biyu da shayarwa abinci ne mai nagarta ga lafiyarku da yaranku. Hanta na kara lafiyar mahaifa da kare zubewar ciki.
Masu ba da jini to sai su fake cin hanta da ganye da kuma shan maltina wannan zai kara ninka muku jini a jika.
-Idan aka girka hanta da tafarnuwa to an samu wata dama ta hadin wani magani na musamman da zai magance cututtuka daban-daban a jiki kama daga :==================
-Sanyi.
-Hawan jinni.
-Narkarda mugun kitse mai lahani ga jiki.
-Rage guba ko duk wani abu da ke iya cutar da ciki, jini da tsoka.
-Karawa jiki karfin guiwar yaki da cututtuka.
-Rage yawan shuga a jiki.
-Magance cutar daji.
– Maganin cututtukan da kwayar cuta ta birus ke haifarwa.
– Kara yawan sha’awa ga jikin mace da namiji.
-Magance cututtukan da ake dauka ta saduwa kamar gonorrhoea.
-Kunburin ciki da yawan iska da kuma maganin basir.
-Kuraje a harshe da wadanda ke tsirowa a cikin baki.
Wani zai ce ai cin hanta sai masu kudi, a nan hantar naira 100 za ta wadatar, ba lallai bane sai an ci an koshi. Dan ita hanta ai kadan jiki ke bukata, dalili a nan ana bukatar abun da zai gina jiki ne, ba carbohydrate ba ce da ake ci kamar tuwo har sai an koshi. Idan aka ci da yawa to jiki zai dibi kadan iya abin da yake bukata sai ya maida sauran kashi dan ba ta da wajen zama a cikin ciki. Dan haka sai a nemi hanta mai kyau a sanya tafarnuwa a girka a ci a sha ruwan. Lalle za a amfana
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment