Friday, February 22, 2019
Karanta, Domin Kasancewa Koda Yaushe Acikin Koshin Lafiya DA Annashuwa
Ni'imar Jiki Da Gyaran Aure::::
MAGUNGUNA GUDA GOMA ATAQAICE KASHI NA FARKO
1.maganin samun hazaqa da basira ga yara :- asamu Zuma wadda batada garwaye ko hadi a riqa digawa yaro abaki idan za'abashi ruwa abashi ruwan zam zam inasha Allahu zai zama mai basira da hazaqa idan yatashi.
2. maganin samun lafiyar jiki :- asamu man
habba da Zuma da man riding (simsim).ahafasu wuri daya arika sha safe da yamma duk Wanda yatsare haka zai sami lafiyar jiki da ikon Allah.
3:- maganin yawan zazzabi asamu ganyen na'a na'a da sassaqen zaituna a hadasu wuri daya a tafasa a riqa sa Zuma asha safe da yamma za'asamu waraka da yardar Allah
4. maganin samun kariya daga jinni:- a saba da karatun suratul falaq da nasi , sai asamu garin warakatu da hantiti ahadasu wuri data arika diba da babban cokali biyu asa ga ruwan dimi ,ariqa sha safe da yamma adage dayin haka za"a sami kariya da ikon Alllah.
5.maganin kunar wuta :- asami Zuma wadda batada hadi ko garwaye sai a wanke wurin ashafa ,kullum kafin a karya asha Zuma za"a samu waraka da ikon Allah.
Admin maijidda Bello ✍️
6.maganin ciwon hakarkari ko awazzu.:- asamu sayen anza da kimba adakesu a shafa idan za"a sha sai ajika sayen anza ko garin anza da ikon Allah za'a sami sauqi.
7.maganin fitar fararen ruwa ga al'aura (sanyi kenan). :- asamu garin hulba da garin tini ana sawa a ruwan dimi asha da safe da yamma za'a samu waraka da ikon Allah.
8.maganin hawan jini:- asamu kaucin dogonyaro (darbejiya)adakeshi a riqasha da nono safe da yamma tsawon kwana goma sha biyu.
9. maganin ciwon haqora::-asamu jibda da ruwan khal. ahadasu wuri daya arinqa digawa a hauren koda yayi kogo haka za'a dingayi da ikon Allah za'a samu waraka.
10.maganin karfin mazakuta .:- asamu garin habba da lubban zakari da man habba,man jir-jir da Zuma ahadasu wajai ddayaarika shan cokali daya kullum da safe da yamma .Allah shine da magani .Wanda ya karanta yayimani addu'a .
Note idan aka kira na miji ne zai dauka ba mace ba
Layin shago ne wanann ba na admin maijidda Bello
Admin maijidda Bello ke yi muku fatan alkairi
Ni'imar Jiki Da Gyaran Aure
Magunguna guda goma kashi na biyu
11-- maganin ciwon zuciya
-asamu garin zaitun da garin jir--jir ahadasu wajai days asanya ruwa kadan da Zuma ahada da ruwan kal arika SHA safe da yamma .
12--Meaganin qarfin gamsuwa ga ma'aurata.
asamu fan no mai kyau da kwakwar ruwa arika niqesu ko malkadewa wuri daya asa madara asha za'aji gamsarwa insha Allahu.
13---maganin raunin mazaquta.
Asamu tafarnuwa cokali biyar garin habbatus saudat cokali ukku citta cokali itacen dan kamaru da hizigar doka cokali ukku da Zuma Kofi daya sai a hadesu wuri daya a riqa shan cokali ukku a yini.
14.maganin rashin yin bacci .
a had a garin tafarnuwa da madara ayi shayi dasu da ikon Allah bacci zaizo bada jimawaba insha Allahu.
15.maganin basir.
a hada malga, faru, hano,nunu da kamdare a riqa sha za'a dace insha Allahu.
16.maganin wahala wajan fitsari.
Asamu tafarnuwa ,hulba , jauzuldi a tafasa a rinqa sha da Zuma za'a samu sauki da yardar Allah.
17.maganin gudawa.
A jija garin tafarnuwa bayan ya jika sai a zuba Zuma cokali biyu a shanye, Indian bai tsayaba ,sai a sake maimaitawa har a samu sauki.
18- Meaganin ciwon asma
Ahada garin tafarnuwa da Zuma da fijil karamin cokali a rika shan cokali biyu a yini, za a samu dacewa da ikon Allah.
19. maganin hawan jini 2
Asamu garin tafarnuwa cokali ashirin garin habbatus saudat cokali goma Zuma lita daya a hadesu guri daya a rika shan cokali biyu sau ukku a yini za'a dace da ikon Allah
20. maganin diabetics.
ahada tafarnuwa cokali goma sha biyar da hulba cokali biyar murdan kankane, tsada rabin kwano madaci gongoni daya a cikin madara asha dasafe kafin akarya kumallo za'a dace insha Allahu.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment