Friday, February 22, 2019

Auren Zumunci Na Daa, Da Na Yanxu


A shekarun baya da suka shude a zamanin iyayenmu da kakanninmu a nan kasar Hausa harma da wasu sassan kabilun Nijeriya mafi akasarin auratayya anfi yin auren zumunci. Inda za ga ka iyaye ne ko kakanni suke hada wanna auren, walau a iya dangin uwa ko dangin uba ko kuma a tsakanin bangaren yan uwan juna. Kai a wancen lokacin harma a zaman makotaka ko zaman garin daya ko abota a tsakanin iyaye takansa su hada ‘ya’yansu auren zumunci koda kuwa su ‘ya’yan basu san juna ba. A haka za a hada wannan auren tare da kowa yana so kuma a zauna lafiya a yi ta rayuwa har illah masha Allahu.\


Daga baya ne ma abun ya koma saurayi zai iya ganin budurwa a cikin dangin babansa ko ma mahaifiyarsa ya nuna yana son ta kuma take a nan yarinyar ta amince har lamarin ya kai ga sun yi aure, kowa yana yin farin ciki a tsakanin iyayen da yan uwa da abokan arziki. Haka shima wannan auren za a zauna cikin mutunci da girmama juna.
Auren Zumunci A Zamanin Yanzu:========================
Wasu da yawa daga cikin iyaye sun dauki auren zumunci da cewa yana lalata zumunci, wanda abun ba haka yake ba a zahirin gaskiya. Koda saurayi ya ga rayinya a danginsu yana son ya aure ta, haka itama yarinyar ta amince tana son sa za ta aure shi, to fa a nan za ka ga wasu daga cikin iyayen sun fara bayar da matsala ta rashin amincewar su musamman ma a yi dacen cewa shi wannan saurayin talaka ne bashi da abun duniya.
Magana ta gaskiya, mafiya yawan iyayen a halin yanzu, sune sanadiyyar wargaza yin auren zumunci a kasar Hausa. Domin mafi akasarin matsalolin da ake samu a auren zumunci za ka ga iyaye musamman mata su ne suke haddasa wannan fitina har lamarin ya zo ya lalace gaba daya.

A yanzu haka mallam bahaushe ya mayar da auren zumunci abun kyama a cikin zamantakewarsa, domin a duk sanda aka yi maganar yin auren zumunci za ka ji ana cewa, kai ni wallahi bana son auren zumuncin nan gwanda na je na dauko bare a can waje amma ba a dangiba.

Idan mai karatu zai yi tunani zai yarda da cewa shifa auren zumunci ya fi komai dadi da kuma sauki, domin yanzu idan ka ga yarinya a danginka ka ji kana son ta, to fa ka san komai nata na halayyarta da na iyayenta baka da wata fargaba na sai ka yi bincike a kan ta da iyayenta. Idan mutanen kirki ne ka sani, hakama idan mutanen banza ne ka sani tun da yan uwanka ne.

Haka itama a nata bangaren yarinya da iyayenta basu da wata fargaba a kan ka saboda sun san komai naka.

Hakama a bangaren babban abun da yake wahalar da samarin yanzu wajen yin aure wato lefe, matukar yarinyar ‘yar uwanka ce, to fa iyayenta da ita kanta ba za su baba takura maka ba a kan sai ka yi abun da ya fi karfin ka ba, domin kaima dan su ne.

Dan haka ni ina mai bawa samari da ‘yan mata na wannan zamanin cewa, koda ba za ki yarda da hadin da iyaye za su yi muku ba na auren zumunci ba, to ga wata shawara, a matsayin ki na budurwa wacce ta isa aure ki dinga yawan ziyartar gidajen ‘yan uwanki sosai musamman ma gidan da kika san su na da samari, idan da halima ki dan dinga yin kwana biyu a gidan. Ta haka ne wani dan uwan naki zai gan ki ya ji ya kamu da son ki har ku kulla soyayyar da za ta kai ku ga yin aure.

Haka kuma ‘yan samari ku dinga yawaitar kai ziyara gidanjen ‘yan uwanku musamman ma gidajen da kukasan suna da ‘yan mata da zarar kun dau wanka ku dinga kai ziyara kuna gaisawa, a haka za ka iya gano wacce za ka ji zuciyarka ta kamu da son ta sosai ko kuma ita yarinyar idan tana ganin ka kullum cikin tsafta da wanka mai kyau ta ji ta kamu da sonka, domin kunsan mata yanda suke da son kwalliya shi ya sa namiji dan gayu yake burgesu. Ku kuma iyaye dan Allah da zarar saurayi a cikin dangi ya ga yarinya yana son zai aure ta, dan girman Allah ku cire wannan tunanin na cewa auren zumunci lalata zumunci yake yi. Wallahi auren zumunci karama dankon zumunci yake yi a tsakanin dangi, bawai bata zumuncin ba kamar yanda wasu suke cewa ba. Kowani irin aure yana tare da nashi matsala, bawai auren zumunci bane ked a matsala. Auren zumunci yana kara da saka ma’aurata kusanci tare da tausayin juna, kuma ka ga duk wani abun da ka bawa matar, to kasan cewa ka bawa ‘yan uwarka ce. Hakan zai saka ma’aurata tausayawa juna da kuma kare hakkin juna game da zamantakewar aure. Auren zumunci baya taba lalata zumunci, sai dai yama kara dankwan zumuncin ma. Dan Allah samari da ‘yan mata ku gwada daukan wannan shawarar tawa wajen yin auren zumunci, ko ma za a daina shan wahala a harkar auratayya a kasar Hausa.

No comments:

Post a Comment